Jami'an tsaro a jihar Kebbi sun kama wasu bamabamai da ake ƙoƙarin shigo da su Nijeriya

 Jami'an tsaro a jihar Kebbi sun kama wasu bamabamai da ake ƙoƙarin shigo da su Najeriya sakaye a cikin buhuna da kwalaye.


Jami’an tsaron kan iyaka na Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya Kwastam (NCS) dana hukumar shige da fice ta Nijeriya, Ma’aikatar Harkokin waje da sojojin Nijeriya karkashin jagorancin babban Sufeton Kwastam, A.A. Ibrahim, wanda yanzu mataimakin kwanturola na hukumar Kwastam da ke kan titin Yauri-Jega a jihar Kebbi ya kama kwali 40 da buhuna dauke da ake zargin bama-bamai ne.


Da yake zantawa da manema labarai a jiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Kwanturolan hukumar kwastam na jihar, Iheanacho Ernest Ojike, ya ce bayan gwajin da jami’an hadin gwiwa suka gudanar, an gano kayayyakin da ake zargin dauke da kwalaye 40 da kuma buhuna guda 6,240 na bama-bamai waɗanda akai lodi a kan farar Canter/ babbar mota mai lamba Zur 882ZY tare da lambar babur Haejue JEG-562 UQ.


Kwanturolan ya ce an kama wasu mutane biyu da hukumar kwastam ta tsare su a Birnin Kebbi tare da mika kayayyakin da aka kama ga jami’an tsaro na jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post