Masara ta fara komawa daidai aljihun talaka a Nijeriya


A wannan makon dai, Masara ta fi sauki a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa sama sauran kasuwannin Sassan kasar nan, inda ake sayar da buhun Masara N45-47,000, bayan da makon da ya gabata aka sayar akan kudi N55-57,000, an samu sauƙin N10,000 daidai a wannan makon.

Ita ma dai Kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuɗin Masarar ta kara sauka a satin nan, a makon da ya shude an sayar da buhun masarar kan kudi N62,000, yayin da a makon nan ake sayarwa kan kudi N54,000.

A kasuwar Kashere a jihar Gombe, an saida buhun masara N45-50,000 a Mako na biya kenan cikin watan Shawwal, Saɓanin na makon jiya da aka sai da N56-58,000 a kasuwar.

Hakazalika Farashin Buhun Masarar ya sake sauka makon nan a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da aka sayar N58000, yayin da a makon da ya wuce aka sayar N60,000 an samu sassaucin N2000 kenan a kasuwar.

Ana dai ci gaba da samun rahusar kayan abinci a wannan makon, Inda ake sayar da buhun masara N60,000 cif a Kasuwar Mile 12 International Market dake Legos, bayan da makon da ya gabata aka sayar kan kuɗi N63,000.

A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, kudin buhun Masara a makon nan N,53,000 ake saidawa, yayin da a makon jiya aka sayar N55,000.

A bangaren Shinkafar Hausa kuwa, ta fi tsada a kasuwannin jihohin Kaduna da Adamawa, inda ake sai da buhun N125,000 a kasuwannin, sai dai farashin buhun Shinkafar na makon da ya gabata ya sha banban a kasuwannin, an sai da buhun, N136,000 a kasuwar Girie da ke jihar Adamawa a makon da ya shude, ita kuwa kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, N130,000 aka sai da a makon da ya gabata.

An sai da buhun Shinkafar Hausa N105-115,000 a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, Sai dai a makon jiya N120-130,000 ne kuɗin buhun Shinkafa a kasuwar.

Ita ma dai kasuwar Mile 12 International Market a jihar Legas farashin Buhun Shinkafar ya sake sauka a satin nan, ana sayar da Shinkafar Hausa N120,000, amma a makon da ya wuce N130,000 aka sayar an samu sauƙin N10,000 a makon nan.

Shinkafar Hausar ta fi sauki a makon nan a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da aka sai da buhun N105,000, bayan da a makon da ya kare aka sayar N110,000
Nan ma an samu ragowar N5000 kenan a makon da ke shirin karewa.

Sai dai kuma Farashin buhun Shinkafa 'yar gida ya ɗan tashi a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano da aka sai da buhun N113,000 a makon nan, yayin da a makon da ya shude aka saida N110,000 daidai.

To a bangaren Shinkafar Bature kuwa, ta fi tsada a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, inda ake sai da buhun kan kuɗi N70,000 a satin nan, sai dai fa duk da haka farashin ya fi sauki kan na makon jiya da aka sai da N78,000.

Haka nan Shinkafar Baturen N68,000 ake sayarwa a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, amma a makon da ya kare an sayar da buhun kan kuɗi N70,000 daidai a kasuwar, an samu sauƙin N2000 kenan a makon nan.

N62-63,000 ake sayar da buhun shinkafar waje a kasuwar Kashere da ke karamar Hukumar Akko na jihar Gombe, sai dai kuma N75,000 aka sayar da buhun a makon da ya shude, an samu canjin N12,000 kenan a mako ɗaya kacal a kasuwar.

Ita kuwa Kasuwar Dawanau da ke jihar Kano an samu karin N1000 guda kan farashin buhun Shinkafar na baya, da aka sai da N62,000, amma a makon nan an sayi buhun Shinkafar Bature N63,000.

Hakazalika a kasuwar Mai'adua jihar Katsina an samu kari a farashin shinkafar waje a makon nan da aka sayar N62,000, inda makon da ya wuce aka saida N58,000, an samu karin N4000 kenan.

To bari mu kammala Farashin Shinkafar Baturen da Kasuwar Mile 12 International Market dake Legos, an sayi buhun Shinkafar N65,000 a kasuwar, a wannan da ke dab da ƙarewa,bayan da a makon daya gabata aka sayar N63,000, hakan na nuni da cewa an samu karin N2000 kenan a wannan makon nan.

Ga ma'abota cin Taliya kuwa, Spaghettin ta fi tsada A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, inda ake sai da ko wani kwali na tafiyar N14,500 a makon da ya shude, Yayin da a makon nan aka sai da N14,000 daidai.

A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano,farashin kwalin a wannan makon N13,000 ne,sai dai a makon jiya N13,500 ne kuɗin Kwalin taliyar,

Kwalin Taliyar tafi sauki a kasuwar Kashere dake jihar Gombe a makon nan,da aka sayi kwalin N12,600,yayin da a makon daya gabata aka sayar N13,000 cif,an samu sauƙin N400 kenan a makon.

Bayan da DCL Hausa ta leka kasuwar Mai'adua jihar Katsina kuwa,ta taras da cewa 
Farashin kwalin taliyar sake Hawa ya yi a kasuwar,inda a makon jiya aka sai da N12,000 daidai,sai dai a makon nan N13,500 ake sai da kwali guda na taliyar.

Ita kuwa kasuwar Zamani dake jihar Adamawa farashin kwalin taliyar bai sauya zani ba,inda a makon daya gabata ake saidawa kan kuɗi N13,000 daidai,haka nan aka sai da a makon dake yi mana bankwana.

To bari ƙarƙare farashin kayan abincin na wannan makon da farashin Taliya a kasuwar Mile 12 International Market Legos dake kudancin kasar,inda kuɗin kwalin ya kama N13,500, sai dai fa wannan makon an samu sauƙin N1000 guda kan farashin makon jiya da aka sai da N14,500.

DCL HAUSA A'isha Usman Gebi.

1 Comments

Previous Post Next Post