Masu ruwa da tsaki a APC sun bukaci Ganduje ya yi murabus

 Masu ruwa da tsaki a APC na son Ganduje ya yi murabusWasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da suka fito daga shiyyar Arewa ta tsakiya sun rubutawa kwamitin ayyukan jam'iyyar na kasa (NWC) inda suka neman shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus.


Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mohammed Mahmud Saba ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.


Inda tuni aka aika kwafin wasikar ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.

Post a Comment

Previous Post Next Post