'Yan bindiga sun hallaka mutane da rana a kauyen KatsinaWasu mahara da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun harbe har lahira mutane kusan biyar a Unguwar Ango dab da kauyen Pauwa na karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce mutanen sun bar garin na Pauwa ne a ƙoƙarinsu na gudun hijra zuwa garin Kankara bayan da hare-haren 'yan bindiga suka addabe su.

Majiyar DCL Hausa ta ce dama 'yan bindigar sun ja kunnen mutanen garin Pauwa da kada su kuskura su yi gudun hijra zuwa wani gari, har ma 'yan bindigar suka lashi takobin cewa duk wanda suka kama na yunkurin aikata hakan, a bakin ransa.

Sai dai bayanai sun ce mutanen yankin na bin lunguna a kauyukan da ke makwabtaka suna zillewa don su tsira da rayuwarsu.

Wasu bayanan ma sun ce an ga gawar wani mutum da ake kyautata zaton 'yan bindigar ne suka harbe shi, a kan hanyarsa ta zuwa Kankara daga Pauwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post