DSS sun kama wata 'yar APC mai goyon bayan tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i biyo bayan wani rubutu da ta yi a shafin Facebook.

 DSS sun kama wata 'yar APC mai goyon bayan tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i biyo bayan wani rubutu da ta yi a shafin Facebook.


A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an tsaro da ake kyautata zaton jami’an tsaron farin kaya ne na hukumar DSS ne suka kama wata ‘yar siyasa mace kuma ‘yar jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Aisha Galadima.


An ce kamen na da nasaba da wani sako da aka wallafa a kafafen sada zumunta na yanar gizo game da gwamnan jihar, Uba Sani.


Wata majiya ta bayyana cewa, Galadima ta soki kalaman Uba Sani na karshe akan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.


Wata makwabciyarta ta ce an kama ta ne a unguwarsu da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi da yamma, sedai tun bayan daukan ta wayanta akashe yake ba asamu ji daga gareta ba. 


Sai dai babban sakataren yada labarai na gwamnan Jihar, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bai da masaniya game da kama ta, kuma ya mika wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS karin haske kan lamarin kamar yadda ya shaidawa Jaridar Daily Trust.

Post a Comment

Previous Post Next Post