'Yan bindiga sun bude wa motar fasinja wuta a kauyen Katsina


Wasu mahara bisa babura sun bude wuta ga wata motar fasinja dauke mutane da mafiyawansu 'yan yawon sallah ne a titin Yantumaki zuwa Danmusa a jihar Katsina

Majiyar DCL Hausa ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:36 na ranar Asabar din nan.

Sai dai bayanai sun ce 'yan bindigar ba su yi nasarar kashewa ko raunata kowa ba a cikin motar. Amma majiyar ta ce razani ya sa wasu daga cikin fasinjojin sun ji raunuka.

Bayanai sun ce motar kirar Golf mai launin ja, na dauke da fasinjoji kusan 10, da ta tashi daga Sabuwar Tasha a cikin kwaryar birnin Katsina zuwa garin na Danmusa.

Rahotanni sun ce a karshe-karshen azumin Ramadana har zuwa shagulgulan sallah kusan duk rana sai barayin dajin sun tare hanyar Yantumaki zuwa Danmusa, ko dai su bude wuta ga matafiya ko su sace wadanda suka yi nasarar kamawa.

Tsakanin garin Yantumaki zuwa Danmusa dai na da nisan kilomita 17.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya ce zai tuntubi babban baturen 'yan sanda na karamar hukumar Danmusa don jin yadda abin ya kasance, amma har lokacin hada wannan labarin, DCL Hausa ba ta samu martaninsa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post