Neman suna kungiyar NEF ke yi - Shugaba Tinubu na son arewa in ji minista Matawalle

Neman suna kungiyar NEF ke yi - Shugaba Tinubu na son arewa inji minista Matawalle 

Ministan kasa a ma'aikatar tsaro ta Nijeriya Bello Mohammed Matawalle ya ce wadannan mutanen da ke kiran kansu dattawa a arewacin Nijeriya, su na yi ne ba don yankin ba, sai don neman suna a siyasance.

A cikin wata sanarwa da ministan ya sanya wa hannu da DCL Hausa ta samu kwafi, Bello Matawalle ya ce mutanen na yin wadannan kalamai ne kawai don su haddasa rudani, rarrabuwar kai da jefa shakku a zukatan 'yan Nijeriya.

Ministan na martani ne kan kungiyar dattawan arewacin Nijeriya da ake kira NEF, wace da farko ta soki lamarin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu cewa ba ta amfanin gwamnatin Muslim-Muslim ticket ba.

Sai dai a cikin sanarwar Minista Bello Matawalle ya ce wadannan mutane ba su da wani tasiri a yankin, asali ma, ba yankin arewar ne a gabansu ba.

Ya ce dan takararsu da ya sha kaye a zaben 2023 ne ya sa suka fito suke wadannan maganganun don su kawar da hankalin 'yan Nijeriya daga irin abubuwa ci gaban da shugaba Tinubu ya fara assasawa.

Bello Matawalle ya ce NEF da ke kiran kansu dattawa, sai ga shi sun gaza samar da hadin kai a yankin na arewa. 

Ministan ya ce har yanzu ba kungiyar ba ta taba ziyartar wani minista da sunan su na so a tattauna batun tsaro, aikin gona, lafiya, ilmi da sauran batutuwan da suka shafi yankin ba domin sanin inda aka dosa a harkar aikin gwamnati.

Ya ce mafiyawansu sun fi son ganin laifin gwamnati don su yi suna.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp