Ganduje da matar sa zasu gurfana gaban kotu ranar 17 ga wannan wata na Aprilu

Wata babbar kotu a jihar Kano ta sanar da ranar 17 ga watan Afrilun wannan shekara a matsayin ranar da tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a yanzu, Abdullahi Ganduje da matar sa da wasu mutane shida za su gurfana a gaban ta bisa zargin su da aikata laifuka har kashi takwas da suka haɗa da na karkata wasu kuɗaɗen gwamnati da almundahana da ma batun karɓan cin hanci na dalolin Amurka da aka yi wa tsohon gwamnan Ganduje.

Kwamishinan Shari'a na jihar Kano Haruna Isa Dederi ya tabbatar da cewa an kammala hada dukkan takardu kan wannan Shari'a kuma za'a tura sammaci ga dukkan waɗanda ake zargi.

Kwamishinan Shari'a na Kanon ya ce abin da Ganduje bai fahimta ba shine bazai iya shã ba a wannan tuhume-tuhume, da yake fadin wai gwamnatin Kano bazata iya gurfanar da shi tare da kama shi da laifi ba saboda yana tãƙamar shi shugaban jam'iyyar APC ne na ƙasa, to amma ya sanī cewa wannan batu ne da ya shafi harkar jiha ba taraiya ba.

Yan kwanaki da suka wuce an jiwo Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano yana alwashin sai ya binciki Ganduje, saboda abin kunya da ya ce ya haifar wa jihar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp