Mahauci ya daɓa wa matar sa wuƙa a dalilin wayar salula
Wani mahauci yayi sanadin mutuwar matar sa bayan caka mata wuƙa da yayi bila adadin a bayan ta saboda daukar wayar sa ta salula da ya ce ta yi.

Rundunar yan sanda a jihar Adamawa ta tabbatar da faruwar lamarin a Sabon Gari-Futy da ke ƙaramar hukumar Girei, inda a cewar sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ta yan sandan jihar Adamawan ta fitar ke nuna cewar mijin matar mai suna Ibrahim Abubakar ɗan kimanin shekaru 33 a Duniya, shi ya fallasa kansa da kansa yana faɗin cewa yayi nadamar kashe uwar ɗan su guda.

Rundunar yan sandan ta ce an samu nasarar kama shi ne bayan sanar da ita wannan mummunan al'amari da mahaifin matar yayi, da kuma wasu bincike da aka gudanar da suka bada dãmar gano makami da yayi kisan da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post