Abin da ya kamata ku sani dangane da Zakkar Fida-da-Kai tare da Sheikh Daurawa

 


((Daga shafin Facebook na Malam Daurawa))

ZAKKAR FIDDA KAI A CIKIN SAUƘI
Tambaya, Maicece zakkar fidda kai?
Amsa : Zakkar (kono) fidda kai, itace zakkar da a ke fitarwa duk shekara, a ranar ɗaya ga watan shawwal wato ranar salla.
Tambaya : Mainene Hukuncin ta?
Amsa : Hukuncin zakkar fidda kai, wajibi ce akan dukkan musulmi, namiji ko mace babba ko ƙarami.
Tambaya : Mainene Hikmar zakkar fidda kai?
Amsa : Hikmar zakkar fidda kai, tana da yawa daga ciki, akwai:
1. Tsafta ce da tsarkake mai azumi daga maganganu da aiyuka mara sa amfani da suka faru a gare shi a watan azumi.
2. Bayar da tallafi da taimako na jinƙai ga marasa ƙarfi.
3. Tana tsaftace jiki daga nauyin zunubi wanda ya rage, wanda a azumi bai kankare ba.
4. Nuna godiya ce ga Allah (ta’ala) bisa ni'imar gama azumi lafiya.
5. Ƙara yawan lada ne a kan wanda aka samu a cikin azumi.
6. Nuna farin ciki ne ga kowa yadda ko wanne talaka ya sami tuwan salla.
Tambaya a kan wa wannan zakkar ta wajaba?
Amsa : Ta wajaba a kan dukkan musulmi namiji ko mace, babba ko yaro. Bawa ko ɗa, Mai hali
Tambaya : Yaya ake gani mai hali da mara hali wajan yin zakkar?
Mai hali shi ne, wanda ya ke da abincin da zai ishe shi ranar salla shi da iyalin sa, abin da ya yi ragowa sai ya fitar da shi,
Tambaya : Shin Wanda ake bi bashi zai iya zakkar fidda kai?
Amsa: Idan bashin lokacin sa bai zo ba zai yi zakka, amma idan lokacin biyan bashin ya yi sai ya biya bashin, idan ya sami ragowa sai ya yi zakkar.
Tambaya : Shin uba zai fitarwa yayansa ƙanana zakkar.?
Amsa : Uba shi ne zai fitarwa ƴaƴansa ƙanana da zakkar fidda kai, manya kuwa kowa idan yana hali ya fitarwa kan sa.
Tambaya : Shin Mai bayi shi zai yi musu zakkar fidda kai?
Amsa: Idan mutum ya na da bayi marasa shi sai ya fitar musu tun da suna ƙarƙashin ikon sa.
Tambaya : Shin Miji ne zai fitarwa matarsa zakkar fidda kai?
Amsa. : Asali kowa ya fitarwa da kansa, tunda kowa shi ya yi azumin sa, domin wannan zakka ce bata ƙarƙashin ciyarwa, amma idan bata da hali sai ya fitar mata.
Tambaya : Shin za a fitarwa da jariri zakkar fidda kai.?
AMSA. : Idan an haifi yaro a cikin watan azumi ko kafin a saukowa daga idi sai a fitar masa.
Haka idan mutum ya musulunta kafin a sauko daga idi shima idan yana da hali sai fitar tunda ya riski lokacin ta yana musulmi.
Tambaya : A wane Lokacin da ake fidda zakkar fidda kai.?
Amsa: za a iya fitar da zakkar fidda kai a hali uku :
1. Kafin ranar salla, da kwana biyu, wannan fatawa da aikin Abdullahi dan umar.
2. bayan an ga watan salla. Wannan shi ne lokacin da take farawa.
3. Fitar da zakka kafin tafiya idi.
Tambaya wanda bai fitar ba har sai bayan an sako daga idi yaya hukuncin sa?
Amsa: Wanda bai fitar ba sai bayan idi to ta zama sadaƙa, amma bashi da ladan zakka idan da gangan yaƙi fitarwar.
Tambaya : Yaya hukuncin Fitar da zakkar fidda kai bayan an sakko daga idi?
Amsa: duk wanda bai fitar da zakkar fidda kai ba har aka sakko daga idi, to, ta zama sadaƙa, idan sakaci yayi zai sami laifi.
Amma Malikiyya suna ganin har zuwa rana ta fadi a ranar salla za a iya fitarwa, ga wanda bai sami dama ba kafin idi.
Tambaya za a iya rama zakkar fidda kai?
Amsa : za a iya rama zakkar fidda kai.
Tambaya : Wa za a bawa zakkar fidda kai,?
Amsa : Talakawa faƙirai, da miskinai marasa hali, da Wadanda suka cancanci a basu zakka.
Tambaya : Za a iya bawa wanda ba musulmi ba zakkar fidda kai,
Amsa :asali zakkar fidda kai ana bawa musulmi ne, amma ana iya bawa wadanda ba musulmi ba, idan ana maƙotaka da su, domin ciyarwa ce.
Tambaya : Wane Irin kayan abinci ake fitar da zakkar fidda kai daga gare su.?
Amsa : ana fitarwa daga abincin da aka fi yawan samu wanda aka fi ci, a wannan garin, ko a wannan ƙasar, da za a fitar da zakkar, ko wacce ƙasa da irin na su kayan abincin.
14.Yaya Gwargwadon yadda ake fitar da zakkar fidda kai.?
Mudu hudu ake fitarwa ga kowanne mutum daya.
. Tambaya: Shin za a iya bayar ƙima ta kuɗi?
Asali abinci ake bayarwa, amma idan akwai buƙarar bayar da kudin ana iya bayarwa, musamman wadanda suke ƙasashen da babu mabuƙata da yawa, suna iya aikawa da kudi a yi musu a wata Kasar.
tambihi.
An taƙaita hujjojin saboda sauƙaƙawa
Amma a duba :
. 1 ملخص الفقه الإسلامي، للدرر السنية
2. الفقه الميسر في ضوء الكتاب والسنة.
Like
Comment
Share

Post a Comment

Previous Post Next Post