Gidauniyar MaiGemu Foundation ta yi wa marayu 3,000 dinkin sallah


Gidauniyar nan ta MaiGemu Development Foundation da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kankia a majalisar dokokin jihar Katsina Hon Salisu Hamza Rimaye ya assasa, ta sanar da yin dinkin sallah ga yara marayu su kimanin 3,000 a wannan shekarar ta 2024.

Kazalika, Gidauniyar ta kuma sanar da ba da hatsi ga magidanta su kimanin 2,000 da za su yi abincin sallah duk a karamar hukumar ta Kankia.

Bugu da kari, Gidauniyar ta MaiGemu Development Foundation ta sanar da ba da tallafin kudi masu tarin yawa ga masu karamin karfi, 'yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Kankia domin yin cefane da sauran hidindimun sallah da ke tafe.

Wanda ya assasa wannan Gidauniya, Hon Salisu Hamza Rimaye ya ce wannan bikin rabon kaya, shi ne karo na 7 a jere da ya assasa da ake tallafar marayu, masu karamin karfi da sauran mabukata su samu su gudanar da shagulgulan sallah cikin salama.

Ya ce ya yanke shawarar kafa wannan Gidauniya domin rage wa marayu da masu karamin karfi radadin halin matsin rayuwa da mafiyawansu ke shiga musamman idan lokuttan sallah sun gabato.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron hada mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon Faruq Lawan Jobe, kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Hon Nasir Yahaya Daura, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina Bala Abu Musawa da sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp