GWAMNA NAMADI YA DAKATAR DA KWAMISHINAN KASUWANCI, AMINU KANTA.

 GWAMNA NAMADI YA DAKATAR DA KWAMISHINAN KASUWANCI, AMINU KANTA.


Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar A Namadi, ya dakatar da kwamishinan kasuwancin jihar Alhaji Aminu Kanta har zuwa lokacin gudanar da bincike kan shirin ciyar war azumi a karamar hukumar Babura.


Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim.


Sanarwar ta ce matakin wani bangare ne na kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da bin diddigin kudi da kuma tafiyar da kudaden gwamnati kamar yadda aka saba,wadda take nuni da cewa zai cigaba da zama harsai an kammala bincikeA cewar samarwar an dakatar da Kwamishinan ne bisa zarginsa da hannu wajen karkatar da asusun ciyar wa ta buda baki a da gwamnatin ta kaddamar a cikin azumi a karamar hukumar Babura,

Post a Comment

Previous Post Next Post