'Yan ta'adda sun bude wuta a kasuwar Yantumaki sun kashe mutane


Wasu 'yan bindiga da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun bude wuta a kasuwar Yantumaki da ke cikin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a ranar Juma'ar nan.

Majiyar DCL Hausa ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar nan, a yayin da ake tsaka da cin kasuwa, wasu kuma sun fara tafiya masallaci sallar Juma'a.

Bayanai sun ce an ga gawarwakin mutane biyu ciki hada wata mace da aka fasa wa kai har kwakwalwa ta fito.

Kazalika, bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce mutane da dama sun samu raunuka a yayin da suke gudun tsira da rayuwa. Sannan an yi asarar duniya mai tarin yawa.

Sai dai 'yan bindigar ba su dauki dogon lokaci ba,  su na fara harbi ba kakkautawa suka ranta a na kare suka tsere, kafin jami'an tsaro su kawo dauki.

Kasuwar Yantumaki da ke cikin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina dai na ci ne a dukkanin ranar Juma'a ta kowane mako.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani daga hukumomi game da wannan batu.

Post a Comment

Previous Post Next Post