Na ware N4.2m ga matasa masu amfani da soshiyal midiya su yi cefanen sallah - Engr Surajo Yazid Abukur

Tun bayan ganin wani rubutu na Aisha Mashi sai abubuwa da yawa suka dawo man sabbi a kwakwalwata.

Na fara tuna irin yadda matasanmu masu amfani da kafafen sadarwar na zamani suka rika taka muhimmiyar rawa wajen samar da kungiyoyi da take na Tallata manufofin Jami'iyyar APC a bangare na matasanmu sun shiga gwagwarmayar tallata manufar Jami'iyyar APC a karkashin taken *Mun Gani a Kasa Dikko Sabon Shafi* da *Masari ba Rabo da gwani ba* da sauran nau'ukan tallace-tallace da masu jawo hankali.

 Ko shakka babu masu amfani da kafar social media a wannan zamani su ne gishiri na siyasa, domin su ke taka rawa wajen saka siyasa ta yi armashi ko kuma akasin haka. Suna taka muhimmiyar rawa wajen yada ayyukan gwamnati da kuma kareta tare da tallata manufofinta gwamnatin Jami'iyyar APC da kudurorin ta. 

Wannan ya sa koyaushe nake gaza mantawa da ranar 5/12/2022 lokacin da tawagar yakin neman zaben Malam. Dikko Umaru Radda ta kaddamar da yakin neman zabe a garin Faskari da yawa daga cikin matasanmu masu amfani da wannan kafa suna daya daga cikin wadanda suka yi zandi suka isa wannan karamar hukuma aka fara kaddamarwa tare da su. 

Haka ma a ranar 11/12/2022 a garin Daura wajen yakin neman zaben Jami'iyyar APC, sai da na gana tare da zantawa da tarin matasan da ke amfani da kafafen sadarwar na zamani inda na kara masu kwara wa juna kwarin guiwa tare da jawo hankalinsu kan yadda za su cigaba da tallafawa wannan Jami'iyya ta APC wajen yada manufarta da kuma jawo hankalin mutane su zabeta. 

A wannan ranar mun ci abinci tare da su da kuma tattauna irin yadda jami'iyyar APC ke samun karbuwa.

Ranar 19/1/2023 ita ce rana da ta zama wani babin tarihi a game da matasanmu masu amfani da kafafen sadarwar na zamani domin a ranar tawagar yakin neman zaben gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Umaru Radda ta sauka garin Sabuwa. Na tafo da motata na iso garin Sabuwa na tarar da tawagar ta riga ta wuce wasu mazabu da ke da hatsarin shiga, ga kuma matasanmu masu amfani da wannan kafa a farkon garin Sabuwa duk an barsu, suna jira tawagar ta fito, daga zuwa na suka yi kuwwa "ga Kwamnada" nan take na amsa na yi Shahada na jagorance su muka shiga cikin daji domin tarar da tawagar dukkaninsu cikin bugun zuciya tare da karawa juna kwarin guiwa.

Wannan kokari na matasan media tabbas wani abun a yaba ne. Don haka ba za a taba mantawa da su ba, kuma muna tare da su kamar yadda mai girma gwamna ya zabi kusan mutum 70 daga cikinsu ya basu mukamai domin yabawa da kuma kara masu kwarin guiwa na ayyukan su.

Ina sanar da matasanmu masu amfani da wadannan kafafe cewa, gwamnatin jihar Katsina ba zata taba mantawa da su ba.

Amma dai ni a nawa bangaren zan zabi masu amfani da wannan kafar akalla mutane 200 in basu kudin cefane Naira dubu goma-goma (10,000) domin kara masu kwarin guiwa da kuma tabbatar masu da cewa muna tare da su dari bisa dari kuma mu da su duk abu daya ne.

Zan dauki mutane 25 masu taimaka wa gwamna a manyan ma'aikatun jihar nan da kuma mutane 11 masu taimakawa Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua sai mutane talatin-talatin (90) daga kananan hukumomi uku da suka kasance mazabata wato Rimi da Charanci da kuma Batagarawa.

Haka kuma zan zabi mutane goma-goma (20) daga shiyar Funtua da Daura wadanda suke amfani da wannan kafa. Sai mutane 21 fitattu daga shiyar Katsina ta tsakiya. Kazalika zan bayar da kudin cefanan ga mutane 10 da suka kasance abokai garemu da ke aiki a kafafen sadarwar na gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu (Print and Broadcast media)
Sai kuma wasu kafafen sadarwar na zamani guda 10 da suka bayar da gudumuwarsu wajen ganin an kafa wannan gwamnati cikin aminci.

Kazalika suma iyayyenmu da suka dade a wannan kafa zan zabi goma daga cikinsu domin basu na cefanan Sallah na dubu goma-goma (10,000) domin kara masu kwarin guiwa.

Daga karshe suma wasu daga cikin shugabanin Jami'iyya ta ta APC a matakin karamar hukuma da Jiha na kananan hukumomina na Rimi da Charanchi da Batagarawa su 198 za su amfana da dubu goma-goma kudin cefane sai karin mutane shidda za su amfana da dubu hamsin- hamsin. Wanda jumullar kudin da za a raba baki daya zasu kama *Miliyan Hudu da dubu dari biyu da ashirin (N4,220,000)* 

 Muna fatan mu yi tawassali da ayyukanmu wajen rokon Ubangiji ya zaunar da Jiharmu da kasarmu lafiya, ya taimaki mai girma gwamna Malam Dikko Umaru Radda wajen tafiyar da gwamnatinsa lafiya, muna fatan ku saka mu a addu'o'inku Allah ya biya mana bukatunmu ya bamu dacewa da daren Lailaitul Kadari.

Insha Allah daren 27 ga watan Ramadana kowa zai samu kudin sa a asusun ajiyar da ya bayar ta hannun wadanda suka tuntube shi. Da fatan mun sha ruwa lafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp