N66,000 a Kasuwar Dawanau dake jihar Kano,wanda aka sai da N75,000 a makon da ya gabata.
Yayin da a kasuwar Mai'adua jihar Katsina ake sayarwa N62,000 a wannan makon, amma a wancan satin N65,000 ne kuɗin buhun Shinkafa 'yar waje a kasuwar.
Sai dai kuma Shinkafar wajen tafi tsada a kasuwannin jihohin Adamawa da Gombe da ke makwabtaka da juna, inda aka sayar da Buhun Shinkafar Baturen N82-83,000 a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe a wannan makon, yayin da a makon da ya shude kuwa aka sai da N75,000.
Ita kuwa kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos, an sayar da shinkafar N75,000 a makon da ya gabata, to wannan satin ma dai hakan take, N75,000
Kuɗin Buhun Shinkafar waje.
A kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa kuwa, Kudin Buhun Shinkafar N80,000 ne a satin nan, a makon da ya wuce kuwa N78,000 aka sai da buhun.
An samu karin N3000 kan kudin buhun Shinkafar a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna a wannan makon, inda aka sayar da Buhun N78,000, a satin nan, a makon jiya kuma N75,000 ne Kudin buhun yake a kasuwar Giwa dake jihar Kaduna.
Shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a kasuwar Dawanau dake jihar Kano,an saida buhun N105,000 a makon nan,yayinda a makon daya gabata ake saidawa N110,000 a kasuwar,an samu sauƙin N5000 kenan a wannan makon.
Haka nan a kasuwar Mai'adua jihar Katsina ma Shinkafar Hausan ta sauka,a makon nan a sayar da kowane buhu na shinkafar kan kuɗi N120,000, yayin da makon jiya kuma aka saya N130,000 daidai, ita ma dai an samu sauƙin N10,000,wanda ake danganta hakan da Faɗuwar darajar CFA a Kasuwannin Duniya.
A kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuɗin buhun Shinkafar bai sauya ba daga N120,000 da aka sai da a makonni biyu da suka shude.
A jihohin Adamawa da Gombe kuwa Shinkafar ta sake tashi a wannan makon, inda a kasuwannin jihar Gombe ake sai da buhun shinkafar N135-140,000 a makon nan, sai dai a makon da ya gabata kuwa an sai da buhun N115-120,000, an dai samu karin N20,000 kenan a wannan satin.
A kasuwar karamar hukumar Girie dake jihar Adamawa kuwa,an sai da buhun shinkafar Hausa N143,000 a makon da ya gabata,haka nan aka sai da a makon nan dake shirin kare wa.
A kasuwar Giwa dake jihar Kaduna kuwa an samu kari kan kudin buhun Shinkafar a wannan satin,an sai da Buhun N130,000,yayinda a makon daya wuce aka saya N128,000.
Masara tafi tsada a wannan makon a kasuwar Kashere dake jihar Gombe,inda ake sai da buhun N60-65,000 a kasuwar,amma a makon jiya kuwa N60,000 cif ne kuɗin buhun masarar.
Ana sai dai buhun Masara N65,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos a wannan makon,inda a wancan satin ake sai da buhun N63,000 ,an samu sassaucin N2000 kenan a satin nan.
N58,000 aka sayi buhun masara a kasuwar Dawanau dake jihar a wannan makon,haka batun yake a makon daya gabata ma.
Farashin buhun masara ya sauka a kasuwar Giwa na jihar Kaduna a satin nan,inda aka sai da buhun kan kudi N57,000,amma a satin da ya kare, kudin Buhun N62,000 ne.
Kuɗin Buhun Masara bai sauya zani a kasuwar Gombi dake jihar Adamawa,inda aka sai da buhun N59-60,000 a makon nan,haka nan aka sayar a makon daya shude.
Haka zalika, a kasuwar Mai'adua da ke jihar Katsina kudin buhun masara bai canza tufafi ba,an sayi buhun N62,000 a makon jiya,haka batun yake a wannan satin da ke yi mana bankwana.
Ga ma'abota cin Taliya kuma,taliyar yafi tsada a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna,inda ake sai da kwalin N14,000 daidai,sai dai an samu saukin N500 kan kudin na makon daya gabata,da aka sayar N14,500.
Sai dai fa Farashin kwalin taliyar a ko wani mako kara sauka yake a kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos a kudancin kasar,inda a makon nan aka sayi kwalin N13,500,bayan da makon daya wuce aka saya N14,000 daidai.
A kasuwar kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe,kuɗin kwalin taliyar N13,300 ne a makon nan,haka nan a satin daya gabata.
A kasuwar Dawanau dake jihar Kano ma kudin kwalin taliyar yana nan kamar yadda yake a makon daya shude,Inda aka saya N13,500,kuma haka farashin yake a makon dake dab da kare wa.
A kasuwar Mai'adua jihar Katsina an samu karin N500 kan farashin kwalin taliyar na baya,an sayi kwalin kan kudi 13,500 a makon daya shude,yayinda a satin nan kuma aka saya N14,000 cif-cif a Kasuwar.
To idan maka je kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa,an sai da kwalin taliya N13,200 a satin da ya kare ,haka yake a makon nan,N13,200 farashin taliyar.
DCL HAUSA A'isha Usman Gebi.