Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da matarsa kotu bisa zargin karkatar da dukiya




Gwamnatin Kano ta maka tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje da matarsa Hafsat tare da wasu mutane 6 Kotu kan zargin cin hanci da rashawa.


Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat Umar, da Umar Abdullahi Umar da wasu mutane biyar a gaban kotu bisa zarge-zarge 8 da suka hada da cin hanci da rashawa da karkatar da wasu kudade da suka shafi biliyoyin nairori.


Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa sauran wadanda ake kara sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp