Dole ne aba wa al'umma kayan agaji domin ana fama da yunwa



Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya ce duk da cewa bai yarda da raba kayan abinci da tsabar kudi a matsayin tallafi ba, halin da ake ciki a yanzu yana bukatar irin wadannan matakan saboda mutane na fama da yunwa.

A wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels, Gwamna Sule ya jaddada mahimmancin magance matsalar yunwa tare da mai da hankali kan hanyoyin da za a bi don dogaro da kai. 


Yace bayar da horon sana’o’i da jarin aiki ga wadanda suka kammala karatu da manoma domin fara sana’o’insu yana da mutukar muhimmanci 


Gwamna Sule ya jaddada cewa koya wa mutane yadda ake kamun kifi maimakon a ba su kifi, yafi muhimmanci ga al'umma shiyasa suke baiwa bangaren mahimmanci.


Sai dai yace da ya zama wajibi a samar da abubuwan jin kai, musamman a lokutan da ake fama da matsananciyar yunwa kamar a wannan lokacin

Post a Comment

Previous Post Next Post