Kotun CCT ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado daga shugabancin Anti - Corruption

 Kotun da’ar ma’aikata (CCT)  ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban hukumar karbar Korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

A ranar Alhamis ne aka gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a gaban kotu bisa zargin saba ka’idojin da’a na jami’an gwamnati, da cin hanci da rashawa,bayyana kadarorin karya, cin hanci da karbar kyaututtuka da dai sauransu.


Kotun ta amince da bukatar mai shigar da kara inda ta umurci wanda ake kara da ya sauka a matsayinsa na Shugaban Hukumar karbar Korafe-korafen al'umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano bisa zargin saba wa tanadin kundin da’ar ma’aikata da kuma Kotu ta CAP C15 LFN 2004 da ke jiran sauraron karar.


Kotun kuma ta bayar da umurni ga Gwamnan Jihar Kano da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da su dauki dukkan matakan da suka dace don nada jami’in da ya fi dacewa da zai karbi mukamin Shugaban riko na Hukumar Korafe-korafen al'umma da yaki da cin hanci da rashawa har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar. 


Ko da yake, wata majiya a gwamnatin jihar Kano ta shaida wa jaridar  SOLACEBASE cewa gwamnati za ta daukaka kara kan hukuncin saboda akwai umarnin kotu da ya hana gurfanar da shi, da kuma tsare-tsare na Code of Conduct Bureau, EFCC da sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post