Tsanar da ake yi wa 'yan sanda na shafar tsaron Nijeriya in ji PCRC

Kwamitin abokai da masu hulda da jami'an 'yan sanda ta PCRC ta hannun shugabanta Magaji Olaniyan ta yi kira da a kawo karshen abin da ta kira da irin tsanar da ake yi wa jami'an 'yan sandan Nijeriya.

Olaniyan ya ce akwai takaici cikin wannan tsana da ake nuna wa 'yan sanda, da ya ce hakan na shafar batun tsaron da jami'an 'yan sandan ke bayarwa.

Ya yi Allah-wadai da irin nuna kyama da tsanar 'yan sanda da ya ce ana samu nan da can a Nijeriya, inda ya ce kwamitinsu na abokan 'yan sanda zai ci gaba da yaukaka danganta a tsakani.

Post a Comment

Previous Post Next Post