Shugaban Nijeriya Bola ya amince da wasu tsare-tsare guda hudu don inganta fannin ilimi a kasar

Tsarin zai yi wa fannin ilimi garambawul don inganta koyo da bunkasa fasahar zamani.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan al'umma Ajuri Ngelale ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce manufofin da aka amince sun hada da (DOTS),ma'ajin adana bayanai ga malamai, mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta, koyarda malamai fasahar zamani domin inganta koyo da koyarwa.

Mista Ngelale ya ce shirin zai kunshi dukkan makarantu tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantun sakandire.

Post a Comment

Previous Post Next Post