An sake dakatar da Ganduje a APC daga mazabarsa, an ce ba ya biyan kudin harajin jam'iyya

Rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Kano ya sake daukar sabon salo, inda wasu shugabannin jam'iyyar a matakin mazaba suka bulla, inda suka sake sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Solacebase ta ba da labarin cewa sabon tsagin shugabancin jam'iyyar a mazabar Ganduje cikin karamar hukumar Dawakin Tofa sun ce su ne halastattun shugabannin jam'iyyar daaka zaba a 31 ga watan Juli, 2021.

Da ya ke ganawa da manema labarai a Kano, Sakataren jam'iyyar na mazabar Ganduje Ja'afar Adamu, da ya yi magana a madadin sauran shugabannin jam'iyyar 11, ya ce dakatar da Ganduje a jam'iyyar ya zama wajibi biyo bayan zarginsa da yin 'Anti Party' wato yi wa jam'iyya zagon kasa musamman a zaben da ya gabata da ba ta yi nasara ba.

Ja'afar Adamu wanda dan'uwa ne na jini ga tsohon Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje, ya zargi mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa da kitsa wutar rikici da ta yi sanadiyar tabarbarewar lamurran jam'iyyar da yawa.

Sakataren jam'iyyar ya ma yi zargin cewa Abdullahi Umar Ganduje na ya biyan kudin harajin jam'iyyar na 'statutory party dues'. Ya yi zargin cewa wadancan mutanen da ke kiran kansu shugabannin jam'iyyar APC a mazabar, na bogi ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post