Mutun sama da 4000 aka kashe da kuma garkuwa da su a farkon shekarar 2024.


Mutane sama da dubu biyu da ɗari biyar aka kashe, aka kuma yi garkuwa da wasu mutanen fiye da dubu biyu a watanni uku na farkon wannan shekara a Najeriya a cewar binciken da wani kamfanin da ke samar tsaro da kuma tattara bayanai kan lamurran tsaron a Najeriya mai suna Beacon Security and Intelligence limited.

Saidai ƙididdiga da kamfanin ya bayar na nuna cewa kaso 80 cikin ɗari na kashe-kashen da aka yi a arewa suka auku, sa'annan kaso 94 na garkuwa da mutane da aka yi daga watan Junairu zuwa Maris sun auku ne a yankin Arewacin Najeriyar.

Wannan ƙididdiga na kamfanin Beacon Security ya baiyana cewa a kullu yaumin ana kashe rayukan mutane 28, ana kuma yin garkuwa da aƙalla Mutane 24 a kowa ce rana.

Toh saidai wannan himma na gano yawan mutuwa da garkuwa da ake yi da mutane da wannan kamfani ya yi, ya ci karo da bayanan mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro malam Nuhu Ribadu, wanda ya nuna cewa an samu raguwar aukuwar mace-mace da kuma garkuwa da mutane da kamfanin na Beacon ke fadi cewa sun auku a farkon shekarar nan ta 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post