Mu na so ka sake rage Naira 300 a farashin dizil a Najeriya

Bayan zabge Naira ɗari biyu da hamsin (250) a farashin ma'aunin lita guda na dizil, ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya IPMAN ta buƙaci matatar mai ta Dangote ta maida farashin litar ta dizil zuwa Naira ɗari bakwai (700).

Mataimakin shugaban kungiyar a Najeriya Hammed Fashola ya ce tunda yanzu babu maganar biyan kuɗin dakon man a jigin ruwa da kuma biya Kwatsam da sauransu, saboda a gida Najeriya ake haƙo tare da tãce man, akwai bukatar farashin ya sauƙa zuwa Naira 700.

Baya ga nuna farin cikin ƙungiyar ta IPMAN kan ragin Naira 250 da matatar Dangote ta yi a kuɗin na dizil, Mammed Fashola ya kuma ce la'akari da yadda darajar Naira ke ƙaruwa, babban dalili ne na rage kuɗin na dizil zuwa 700.

Matatar man ta Ɗangote dai ta fara rage kuɗin na dizil ne daga Naira 1,600 zuwa 1,250 makwanni biyu da suka gabata, sannan a mako da ya gabata kuma ta sanar da sake zabge Naira 250 a makon jiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post