Ƙirƙirar yan Sandan jihohi zai zama silar ƙãrin sãɓani a tsakanin ƙabilu-Sufeta janar na yan sandan Najeriya

Sufeta janar na yan sanda a Najeriya Olukayode Egbetokun ya ce Najeriya bata kai matsayin da zata yi 'yan sandan jihohi ba saboda za'a riƙa samun umurni daga ɓangarori biyu wato bangaren gwamna da na sufeta janar.

Sufeta janar Olukayode yayi zargin akwai yiyuwar gwamnoni a Najeriya suyi amfani da yan sandan jihohi su wuce gona da iri da kuma take hakkokin yan Adam.

Olukayode Egbetokun ya baiyana cewa jihohi basu da wadãtar da zasu samar da irin 'yan sandan da ƙasa ke bukata domin a kowace shekara ana buƙatar ɗaukar sãbin yan sanda dubu 30 kamar yadda majalisar ɗinkin Duniya ta bukaci a yi dan samar da 'yan sanda na zamani.

Ya ce maimakon kirkiro yan sanda na jihohi, ƙãra gwamnati ta haɗe jami'an tsaro na civil defence dana hukumar kare haɗura ta ƙasa road safety wuri guda da yan sanda, ta yadda civil defence ɗin da jami'an roadsafty zasu zamo wasu sassan rundunar yan sanda.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp