Mun kori biyu daga cikin dakarun mu dan tabbatar da mutunci da kwarewar aikin soja a Nijeriya -kakakin rundunar sojojin Nijeriya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da sallamar wasu daga cikin sojojin ta bayan samun su da laifi dumu-dumu na satar wasu wayoyin lantarki a matatar Dangote a daidai lokacin da ya kamata su kasance a bakin aiki.

Jam'in hulda da jama'a na rundunar sojojin, Manjo janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da korar sojojin biyu Kofur Innoson Joseph da Kofur Jacob Gani bayan gurfanar da su a kotun soji inda suka gagara musanta Laifuka da aka zarge su da aikatawa.

Ya ce an same su da laifin gaza gudanar da aikin su na soja kamar yadda dokar aikin soja sashe na 57 ya tanadar da kuma aikata wasu laifuka irin na farar hula ƙarƙashin tanadin kundin na 114 ƙaramin sashe na ɗaya a kundin dokokin aikin soja mai lamba A20 na shekarar 2004 a Najeriya.

Su dai korarrun sojojin biyu sun shiga hannu ne a sanadin wani mai suna Smart, wanda ya bukaci su raka shi ya ɗauki wadannan wayoyi da aka bari a kamfani, saidai da ya ga alamun zasu shiga hannu sai ya tsere ya bar su da jangwam.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp