Nijeriya za ta karfafa hadin gwiwa da sauran kasashe domin yaki da ta'addanci a Africa.
Shugaba Bola Tinubu ya ce Nijeriya za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da jagoranci wajen daukar matakan dakile ayyukan ta'addanci a Afirka.
Tinubu ya bayyana haka ne a wajen wani babban taron yaki da ta’addanci na kasashen Afirka da aka yi ranar Litinin a Abuja mai taken “Karfafa hadin gwiwar yanki da gina cibiyoyi don magance ci gaban barazanar ta’addanci a Afirka”.
Ya ce an inganta ayyukan yaki da ta’addanci a Nijeriya ta hanyar kafa dokar hana ta’addanci da kafa cibiyar yaki da ta’addanci ta Kasa, NCTC.
Shugaban ya ce, duk da haka dole ne nahiyar Afirka ta bi diddigin abubuwan da ke haifar da ta'addanci ta hanyar gudanar da shugabanci nagari, bin doka da oda, adalci da kuma hada kai.
Ya ce dole ne a baiwa ‘yan kasar tabbacin tsaron lafiyarsu ta hanyar tsare-tsare masu karfi da nufin kawar da matsalar ta'addanci.
Yaki da ta’addanci na bukatar cikakken tsari. Dole ne mu magance tushen abubuwan da ke haifar da tsatsauran ra'ayi, kamar talauci, warewar jama'a, da rashin adalci a cikin al'umma inji Tinubu