Irin ukubar da 'yan fanshon jihar Katsina ke sha kan layin tantance su cikin rana

Wasu dattijai da shekarunsu ya haura 65, galibi da rashin lafiya tattare da su, sun nuna rashin jin dadinsu kan tsarin da ake bi wajen tantance su musamman a garin Malumfashi da ke jihar Katsina.

A ziyarar gani da ido da DCL Hausa ta kai Malumfashin ta gane wa idanunta yadda tsofaffi galibi masu fama da rashin lafiya ke bin layin fiye da mutane dubu 1 cikin tsananin rana.

Wani daga cikin yan fanshon da muka zanta da shi ya bayyana mana yadda ya tarawa kansa bashi, la'akari da yadda yake kashe fiye da Naira 1,500 a kudin mota cikin sama da kwanaki 4 da ya shafe yana zuwa ba tare da ya samu an tantance shi ba.

Ko da wakilan DCL Hausa suka ci gaba da yunkurin jin bahasi, sun lura da yadda yaran wasu tsofaffin ke goyo su sannan su ajiye su kan rashin lafiya cikin tsananin zafin rana a Galadima Primary School da ke garin na Malumfashi.

Kawo yanzu dai an sallami ‘yan fanshon ba tare da kammala tantance su ba tare da ba su umurnin sake komawa ranar Laraba don sake kafa layin da wasu ke fara bi tun da safe.

Post a Comment

Previous Post Next Post