Tinubu ya tafi kasar Netherland domin ziyarar aiki.

Tinubu ya tafi kasar Netherland domin ziyarar aiki.


A yau ne shugaba Bola Tinubu zai fara wata ziyarar aiki a kasar Netherlands domin tattaunawa da firaministan kasar Mark Rutte.


A wata sanarwa da aka fitar a daren jiya a Abuja mai dauke da sa hannun mai bawa ahugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale, ya ce shugaban ya kai ziyarar ne bisa gayyatar firaminista Rutte.


Yayin da yake kasar Netherland, shugaba Tinubu zai gudanar da taruka daban-daban da Sarki Willem-Alexander, da Sarauniya Maxima,da babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya kan hada-hadar kudi don ci gaba kasa (UNSGSA).

Ka zalika Tinubu zai halarci taron kasuwanci da zuba jari na Nijeriya da Dutch, wanda ke da nufin samo damammaki na haɗin gwiwa da tsakanin 'yan kasuwa na Nijeriya da Holland, musamman a fannin noma da kula da ruwa.

Daga baya shugaba Tinubu zai tafi birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na musamman na dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 28-29 ga watan Afrilu kamar yadda sanarwar ta ce.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp