Kishin arewa ya sa Shugaba Tinubu ya ba 'yan yankin mukamai masu muhimmanci - Nuhu Ribadu

 


Shugaba Tinubu na son a shawo kan matsalolin arewa shi ya sa ya nada 'yan yankin mukamai masu muhimmanci in ji Nuhu Ribadu


Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya soyayyar da ke tsakanin shugaba Tinubu da yankin arewacin Nijeriya ne ya sa ya nada mutanen yankin mukamai masu muhimmanci.

Ya ce an yi hakan ne domin a taimaka a shawo kan duk wasu matsalolin da yankin ke fuskanta.

Malam Nuhu Ribadu na magana ne a Sokoto inda ya ce shugaban kasar na sane ya zabo mukamai masu gwabi ya nada 'yan arewa don su taimaki yankinsu.

Ya ce ko talaucin da ke damun yankin na da ban tsoro, inda shugaban kasar a lokacin kafa jami'an gwamnatinsa, ya ce zai yi duk abin da ya dace don ganin an ceto yankin daga halin da ya ke ciki.

Daga cikin mukamai masu gwabin da shugaba Tinubu ya nada 'yan arewa akwai na tsaro, aikin gona, ilmi, harkokin waje da lafiya.

1 Comments

Previous Post Next Post