Farashin kayan abincin waje ya fi sauki fiye da na gida a Nijeriya


A yayin da Dala da CFA ke ci gaba da sauka a kasuwa, ana kara samun rahusa a kayakin abincin da ake shigo da su daga waje. Sai dai fa abincin da ake nomawa a kasar kuwa farashin bai sauka har yanzu.

Inda a wannan satin ake sayar da buhun masara N63,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos,a makonni biyu da suka shude ma haka ake saidawa a Kasuwar.

Ita kuwa Kasuwar Dawanau a jihar Kano kuɗin buhun masarar kara tashi ya yi duk da cewa tashin Dala da ake danganta tashi da tsadar kayan abinci ya sauka, inda a makon nan aka sai da buhun masara kan kudi N62,000, yayin da a makonnin baya aka sayar a N58,000.

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina kuwa masarar ta ɗan sauka a makon nan, an dai sai da buhun kan kuɗi N60,000 a wannan makon na watan Shawwal, bayan da a watan Ramadan kuwa aka saida N62,000, an dai samu sauƙin N2,000 kenan kan farashin makonnin da suka wuce.

Hakazalika, masara ta sauka a kasuwar Kashere da ke Karamar Hukumar Akko a jihar Gombe, an sayi buhun masara N56-58,000 a satin nan, sai dai a sati biyu da suka gabata kuwa an sayar a kan kudi N60-65,000.

Ita ma dai kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna Masarar ta fara sauka, an sayi buhun N57,000 a makon da ya gabata, amma a makon nan N55,000 ake sai da buhun.

To bari mu karkare farashin masara da kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, an sayar da buhun Masara N55-56-57,000 a satin nan, yayin da makonnin da suka shude aka sayar a kan kudi  N59-60,000 cif cif.

Shinkafar waje kuwa ta fi sauki a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan makon da ake sayar da buhun N58,000, yayin da a watan azumi aka sayar kan kudi N62,000, an dai samu ragowar N4000 kenan a 'yan makonnin nan.

Shinkafar wajen ta fi tsada a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da ake sayarwa N78,000 a wannan satin, yayin da a baya aka sayar kan kudi N80,000 daidai.

Ana saida buhun Shinkafar baturen N62,000 a wannan makon a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, amma makonnin da suka gabata an sayar da buhun kan kuɗi N66,000.

A kasuwar Mile 12 International Market dake Lagos kuɗin buhun Shinkafar Bature ya kama N75,000, haka nan aka saida a makonnin da suka shude ma.

Da DCL Hausa ta leka kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa, N70,000 cif ake sai da buhun a makon nan da ke shirin karewa, yayin da a makonnin da suka gabata aka saida kan kudi  N78,000,an samu sauƙin N8000 kenan a wannan makon.

A kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, an saida buhun Shinkafar Bature N82,000 a makonnin da suka wuce,sai dai a makon nan kuɗin buhun ya kama N75,000, an samu ragin N7000 kenan a makon nan dake dab da ƙarewa.

Ita ma dai shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Karamar hukumar Girie da ke jihar Adamawa, an sayar da buhun shinkafar Hausa N136,000 a makon nan, yayin da makon da ya gabata aka saida N140,000 an samu ragin N4000 akan farashin shinkafar na baya.

A kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos farashin buhun Shinkafa a wannan makon N130,000 ne, yayin da makon jiya aka sayar N120,000 cif.

Ita kuwa kasuwar Mai'adua jihar Katsina N110,000 ake sayar da buhun, bayan da makonnin da suka gabata aka sayar N120,000 an kara samun saukin N10,000 kenan a satin nan.

A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa, a makonnin da suka gabata ana sayar da buhun shinkafar N130,000 daidai, Haka nan batun bai sauya zani ba a makon nan .

Ita kuwa Kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, an saida buhun Shinkafar 'yar gida N135-140,000 a makonnin da suka shude, yayin da a makon nan aka sai da buhun N120-130,000.

Ana sai da buhun Shinkafar Hausa N110,000 a satin nan,yayinda makonnin da suka gabata ake saidawa 105,000, hakan na nuni da cewa an samu karin N5000 kenan a makon nan.

A bangaren Taliyar Spaghetti kuwa, ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos, inda ake saida kwalin N14,500, yayin da a makonnin da suka gabata ake sayarwa N13,500.

Ita ma dai kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuɗin Kwalin taliyar bai sauya zani ba,an sai da kwalin N13,500 a makonnin da suka shude,haka batun yake a makon nan dake dab da ƙarewa.

Idan muka yi tattaki zuwa Kasuwar Kashere da ke jihar Gombe kuwa, an saida kwalin taliyar N13,000 a wannan makon, yayin da makon da ya shude ake saidawa N13,300 a Kasuwar.

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina ana sayar da taliyar N14,000 daidai a makonnin da suka gabata, sai dai a makon nan, N12,000 ake saidawa, an samu saukin 2000 kenan a wannan makon.

Yayin da a Kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa ake saidawa N14,500, bayan da a makonnin da suka shude ake sayarwa N14,000 a samu karin N500 kenan a makon nan.

To a kasuwar zamani dake jihar Adamawa kuwa, An sai da kwalin taliya N13,200 a makonni biyu da suka gabata,yayinda a wannan makon ake Saidawa N13,000, daidai.

DCL HAUSA A'isha Usman Gebi

Post a Comment

Previous Post Next Post