Atiku da Wike sun hadu, karon farko tun bayan zaben 2023, sai dai babu tabbacin ko sun gaisa


A karon farko tun bayan zaben 2023, Atiku Abubakar da Nyesom Wike sun hadu wajen guda don taron jam'iyyar PDP.

Sai dai Premium Times ta ce babu tabbacin ko sun gaisa a wajen taron.

Atiku Abubakar dai shi ne tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, yayin da Nyesom Wike ya yi Gwamnan jihar Rivers sau biyu, yanzu kuma shi ne ministan Abuja a gwamnatin APC.

Sauran wadanda suka halarci taron akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Abba Moro da Sanata Aminu Waziri Tambuwal, akwai tsohon Gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam'iyyar ta PDP Ahmad Makarfi, da tsohon Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu, tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da tsohon Gwamnan jihar Plateau Jonah Jang.

Post a Comment

Previous Post Next Post