Fasinjoji sun yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in kwastam a Katsina


Wasu bayanai da DCL Hausa ta tattara sun ce wasu fasinjoji da ke cikin wata babbar motar dakon kaya, sun yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in kwastam a kan titin Katsina zuwa Dankama ta karamar Kaita a jihar.

Majiyar ta ce motar dakon kayan na dauke da mutane zuwa Dankama a lokacin da jami'an kwastam suka yi kokarin tsayar da ita, amma direban bai samu damar tsayawa ba. Hakan ne ya sa wani daga cikin jami'an kwastam din ya yi harbi da bindiga da aka yi zargin ya samu wani daga cikin fasinjojin da ke cikin motar a kugu.

Bayan da hakan ta faru ne direban babbar motar ya samu ya tsayar da motar, fasinjojin ciki suka sauko, suka durfafi jami'an na Kwastam da bayanai suka ce sun yi nasarar kama wanda ake zargi da yin harbin. 

Daga bisani bayanai suka ce, fasinjoji sun yi nasarar kashe jami'in kwastam din.

Sai dai daga bisani DCL Hausa ta samu labarin cewa shi ma wanda ake zargi jami'in na Kwastam ya harba a kugu mai suna Bashir Na-Buzuwa ya rasu.

Bashir mai kimanin shekaru 27 dan asalin garin Doro ta karamar hukumar Bindawa, na zaune ne a Unguwar Zanguna da ke cikin birnin Katsina.

Lamarin ya faru ne da misalin 10:27 na safiyar Larabar nan a daidai kauyen Gamjin Makaho da ke kan titin Katsina zuwa Dankama na karamar hukumar ta Kaita.

Amma jami'in hulda da jama'a na hukumar kwastam a jihar Katsina SC Tahir Balarabe a lokacin da DCL Hausa ta tuntube shi, ya ce za su fitar da sanarwa a hukumance, amma a lokacin ya ce su na kan kokarin yadda za su dauko gawar wanda ya rasa ran nasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post