Matsin tattalin arziki ya sa za a rufe kamfanonin sarrafa giya guda biyu a Nijeriya

 Matsin tattalin arziki ya sa za a rufe kamfanonin sarrafa giya guda biyu a Nijeriya


Kamfanin samar da giya na Nigerian Breweries na shirin rufe kamfanoni guda biyu,hakan nada nasaba ga ɗimbin matsalolin kuɗi da suke fuskanta, kamfanin ya bayyana hakan a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ya fitar.


Abubuwan da ke damun babban kamfanin sun hada da asarar musayar kudaden waje da aka yi a bara, wanda hakan ya sa ba shi da wani zabi illa rufe biyu daga cikin masana'antun.Ya bayyana cewa wani babbar asarar da aka yi kan hada-hadar kudaden waje da ya kai Naira biliyan 153.3 ya sanya Kamfanin Breweries na Nijeriya ya yi babbar asara a bara, tun bayan da ya fara aiki shekaru 77 da suka gabata a kasar.Asarar Naira biliyan 106.3 da aka yi a cikin 2023 ya samo asali ne daga matsalolin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki, rashin daidaituwar FX, da sauransu,kamar yadda kamfanin ya bayyana.


An sanar da kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar abinci da abin sha da ma’aikatar taba sigari da kuma kungiyar masu shayar da kayan sha da taba sigari kan matakin dakatar da aiki na wani dan lokaci a kamfanonin biyu, a cewar takardar.

Post a Comment

Previous Post Next Post