Hukumar NDLEA ta lalata tare da kona kilogram 304,436 na muggan kwayoyi a Lagos

 Hukumar NDLEA ta lalata tare da kona kilogram 304,436 na muggan kwayoyi a Lagos.


Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, ta lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun abubuwa da aka kama daga sassan jihohin Legas da Ogun a ranar talata.


Da yake jawabi a wajen wani bikin da aka lalata magungunan da aka kama a garin Badagry na jihar Legas, shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya ce an lalata haramtattun kwayoyin da aka kama a fili biyo bayan umarnin da kotu bayar.


Daga nan sai ya yi kira da a kara tallafawa jama’a domin ci gaba da kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke yi na dakile illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya.


Marwa ya ce, “Duk da cewa ana gudanar da atisaye na yau da kullun da kuma tsari na kawar da abubuwa masu hadari daga cikin al’ummarmu, amma ana gudanar da lalatar da haramtattun kwayoyi a gaban jami'an kotu abubuwan da suka hada da haramtattun kwayoyi a jihohin da dama. haka kuma a ajujuwa daban-daban kamar su hodar iblis, da tabar heroin, da wiwi, da tramadol, da sauransu.



Ya ce jami’an hukumar ta NDLEA a sassa daban-daban na hukumar ne suka kama su a jihohin Legas da Ogun tun daga watan Janairun 2022 zuwa yau, musamman a tashoshin jiragen ruwa na Legas da filayen jiragen sama da kuma kan iyakokin kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp