Matatar mai ta Dangote ta sanar rage farashin man dizal.

Matatar mai ta Dangote ta sanar rage farashin man dizal.


Makonni kadan da suka gabata, a lokacin da ta fara aiki, matatar mai ta Dangote ta sanya farashin man dizal a kan Naira 1,200.

Yayin da ake fitar da kayayyakin, matatar ta samar a kan farashi na Naira 1,200 ga kowace lita makonni uku da suka wuce.

Hakan ya nuna sama da kashi 30 cikin 100 na raguwar farashin kasuwa a baya na kusan Naira 1,600 kowace lita.

Sai dai a ranar Talata an kara samun raguwar Naira 200 a farashin, inda a yanzu farashin ya kai N1,000.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce rage farashin man dizal zuwa Naira 1,200 zai yi tasiri ga hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.

Ya yi wannan jawabi ne a wata ganawa da manema labarai bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu na bikin Sallar a Legas.

A cewar Dangote, an samu ci gaban tattalin arziki a baya-bayan nan, wanda ke nuni da cewa kasar na kan turba mai kyau bisa matakan tattalin arziki da gwamnati ke dauka a halin yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post