Ana hasashen cewa ambaliyar ruwa za ta shafi jihohin Nijeriya 31 a bana
Gwamnatin tarayya ta rubutawa gwamnoni 31 takardar sanar da su halin da ake ciki na ambaliyar ruwa a jihohinsu tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba na wannan shekara ta 2024.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan hasashen ambaliyar ruwa na shekara ta 2024.
A wajen taron, hukumar kula da ayyukan ruwa ta Nijeriya, an bayyana cewa an ware kananan hukumomi 148 a jihohin Legas, Kano, Delta, da kuma wasu jihohi 28 a matsayin wuraren da ake fama da matsalar ambaliya.
Hasashen da aka samu na shekara ta 2024 na ambaliyar ruwa ya nuna cewa wani bangare na kananan hukumomi 148 a cikin jihohi 31 na tarayya sun fada cikin yankunan da ake fama da matsalar ambaliya, yayin da wani bangare na kananan hukumomi 249 da ke cikin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja sun fada cikin tsaka mai wuya.
Jihohin da ke fama da matsalar ambaliya sun hada da Adamawa, Akwa-Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas , Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe.