Halartar taron Kwankwasiyya ya sa muka dakatar da gwamnan Kano daga jam'iyyarmu - NNPP

 

Tsagin jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin Major Agbo ya sanar da dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano daga cikin jam'iyyar.


A cikin sanarwar da Ogini Olaposi, sakataren jam'iyyar, ya fitar a yayin taron 'yan jarida na wannan Talata a Abuja, tsagin jam'iyyar ta NNPP, ya ce rashin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi shi ne ya sanya su daukar wannan mataki.  


Jaridar The Punch ta ce tsagin na NNPP ya fusata da halartar babban taron jam'iyyar da wani bangare karkashin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya jagoranta da gwamnan na Kano ya yi a ranar 06.04.2024. 


A jawabin Mr. Olaposi, ya ce ba su ga dalilin da gwamnan Kano zai halarci taron na Kwankwasiyya da a ganinsu haramtacce ne ba. Sai dai tuni wasu 'yan Kwankwasiyya suka yi watsi da wannan dakatarwa daga jam'iyyar ta NNPP wacce a karkashinta ne aka zabi gwamnan na Kano da kuri'u sama da miliyan daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post