Gwamnatin APC ce ta nemi bashin N20bn a jihar Zamfara ba ta PDP ba - Gwamnati

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar cewa jimillar kudin da ake magana N14.26bn ba ita ce ta ciyo bashin ba, ta gaje shi ne daga cikin bashin N20bn da gwamnatin da ta gabata ta nema wa jihar.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara Malam Sulaiman Bala Idris da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce babu wani bashi na cikin gida ko na waje da Gwamna Dauda Lawan Dare ya ciyo wa jihar tun da ya hau karagar mulki.

Sanarwar ta ce "muna son mu warware zare da abawa ga ofishin kula da basuka na Nijeriya DMO a rahoton da ya fitar cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ci bashin N14.26bn.

"Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Dauda Lawan Dare, ba ta taba neman bashi ko ma tunkarar majalisar jiha ko ta tarayya da zummar neman bashi ba.

"Na da matukar muhimmanci mutane su gane cewa gwamnatin da ta gabata ce ta nemi bashin zunzurutun kudi N20bn, amma ta gaza karbar kudin duka.

Sanarwar Malam Sulaiman Bala Idris ta ce gwamnatin da ta gabata ta karbi kudi N4bn daga cikin bashin N20bn da ta nema domin aikin filin jirgi na jihar Zamfara, amma ba ta yi abin da ya kamata da kudin ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp