Liman ya sauka daga aikin limanci saboda takaddamar kudi N500,000 a Kebbi

Babban malamin masallacin juma'a na Wala da ke Birnin Kebbi, Alhaji Rufai Ibrahim ya sauka daga mukaminsa sakamakon takaddamar N500,000 da ta shiga tsakaninsa da na'ibinsa, Malam Mamman Na Ta'ala Yahaya. 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Alhaji Ibrahim ya kai karar Malam Yahaya ga hukumar DSS, bayan da ya zarge shi da yin cogen N500,000 daga cikin kudin da ya kamata su raba na kyautar kudin da gwamnan jihar ya ba su, lamarin da ya sanya aka dakatar da shi saboda rashin kai karar ga hukumomin da suka dace. Sai dai daga bisani ya rubuta aje aiki.


Post a Comment

Previous Post Next Post