Dangote ya sake zaftare farashin man dizil, yanzu lita ta koma N940

 Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man dizal da na jiragen sama zuwa N940, N980 akan kowace lita.


Shugaban sashen sadarwa na rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, wanda ya tabbatar da wannan sabon farashin, ya ce hakan ya yi daidai da kokarin da suke yi na rage wahalhalu da matsin tattalin arziki a Nijeriya.



Chiejina ya bayyana cewa sabon farashin N940 ya shafi abokan cinikin da ke siyan lita miliyan biyar zuwa sama daga matatar yayin da farashin N970 na masu sayen lita miliyan daya zuwa sama.


Ya tabbatar da cewe matatar man Dangote ta shiga wani shiri na hadin gwiwa da gidajen mai da mai na MRS, domin tabbatar da cewa masu amfani da man sun samu siyan mai a farashi mai sauki, a dukkan tashoshinsu na Legas ko Maiduguri."


Kuna iya siyan dizal mai ƙasa da lita 1 akan N1,050 da kuma man jiragen sama akan N980 a dukkan manyan filayen jiragen sama da MRS ke aiki kamar yadda ya bayyana.


Ya ci gaba da cewa za a fadada hadin gwiwar ne ga sauran manyan ‘yan kasuwar man.


Idan dai ba a manta ba ko a makwannin da suka gabata Dangote ya sake rage kudin litar man dizal daga 1200,zuwa dubu 1000.

Post a Comment

Previous Post Next Post