Dangin amarya sun hallaka dan bindiga, yayin da suka dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Zamfara

 Dangin amarya sun hallaka dan bindiga, yayin da suka dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Zamfara'Yanwata uwan wata amarya da gungun fasinjoji sun dakile yunkurin yin garkuwa da wani dan ta’adda a jihar Zamfara.


PR Nigeria ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan bindiga suka yi wa iyalan amaryar da wasu matafiya kwanton bauna a hanyar Talata Mafara zuwa Gusau.


Iyalan amaryar sun yi tafiyar ne don siyan kayayyaki da sauran kayan aure a Kano.


Wani ganau da ya zanta da PRNigeria ya bayyana cewa an mayar da martani ne cikin gaggawa, biyo bayan yunkurin ‘yan bindigar na sace fasinjojin.


Duk da cewa daya daga cikin ‘yan fashin ya yi nasarar tserewa, jajirtattun fasinjojin sunyi nassarar kama bindigu kirar AK-47 guda biyu.


Da yake ba da labarin yadda abin ya faru, wani mai shaidar gani da ido ya ce: “A lokacin da ake tafiya kilomita kaɗan daga shingen bincike na jami'an tsaro na Fangal Tama, matafiyan sun ji ƙarar harbe-harbe ta ko’ina abinda yaja hankalin fasinjonin kokarin nemo hanyar da zasu maida martani.

Post a Comment

Previous Post Next Post