Anyi zargin gwamnatin kano nada Hannu wajen zanga zangar da akeyi na nuna rashin amincewa da shugabancin Ganduje.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano ce ke daukar nauyin zanga-zangar da ake yi ta nuna sai ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar.




Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyar  (NNPP) da ke jagorantar gwamnatin jihar Kano ce ke da hannu a zanga-zangar nuna adawa da shi a Abuja.



Sai dai gwamnatin jihar ta musanta cewa tana da hannu a rikicin.

An yi zanga-zangar neman a tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, inda kungiyoyi da jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa ta tsakiya ke kan gaba.



Ganduje a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta hannun mataimakinsa na musamman kan kungiyoyin farar hula, Kwamared Okpokwu Ogenyi, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano na daukar nauyin masu zanga-zanga a tituna, galibi ‘yan Kwankwasiyya ne, wadanda wasu daga cikinsu sun fito ne daga yankin Arewa ta tsakiya. domin neman Ganduje yayi murabus.



Sanarwar ta kara da cewa, “Muna da sahihan bayanai cewa Gwamnatin kano na aiki tare da wasu daga shiyyar Arewa ta tsakiya tare da bayar da makudan kudade ga wasu mutane domin ci gaba da nuna rashin amincewa da shugabancin Ganduje wanda manufasu shine a tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp