Ya kamata NAHCON ta fitar da lokacin fara jigilar mahajjatan Nijeriya zuwa kasar Saudiyya - IHR

Kungiyar nan mai zaman kanta da ke wayar da kan mutane game da aikin hajji mai suna International Hajj Reporters IHR ta bukaci hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON da ta gaggauta sanar da lokacin da za a fara jigilar mahajjatan bana zuwa kasar Saudiyya.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake kiyasin cewa bai wuce kwanaki 10 da za a fara jigilar mahajjatan zuwa kasar Saudiyya daga kasashen duniya da ke zuwa aikin hajjin a kasar.

Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga shugaban kungiyar IHR na kasa Alhaji Ibrahim Muhammad da DCL Hausa ta samu kwafi da ke cewa kusan dukkanin kasashen da ke zuwa aikin hajji a kasar Saudiyya sun rigaya sun sanar da lokuttan da za a fara jigilar alhazansu zuwa can.

Sanarwar ta ce ya zama kamar al'ada ga hukumar ta NAHCON tana sanar da rana da jihar da za a fara kaddamar da jigilar mahajjatan.

"Abin bai yi mana dadi ba, ganin cewa kwanaki kalilan suka rage a fara jigilar mahajjatan da kuma rufe shafin ba da takardar izinin shiga kasa ta visa, amma hukumar NAHCON har yanzu ba ta sanar da ranar da za a fara jigilar mahajjatan Nijeriya ba".

Alhaji Ibrahim Muhammad ya ce manyan kasashe 5 da suka fara sanar da lokacin daukar maniyyatan su ne kasar Indonesia da za a fara daukar maniyyatanta a ranar 12/05/2024. Sai kasashen Bangladesh da Pakistan da suka saka ranar 9/05/2024. Kasar Malaysia kuwa za ta fara jigilar mahajjatan a ranar 11/05/2024. Ghana kuwa ta saka ranar 18/05/2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post