'Yan sanda sun haramta amfani da na'urar cire kudi ta POS ko 'transfer' a caji ofis


Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta sake nanata batun nan na haramta amfani da na'urar cire kudi ta POS da duk wani nau'in tura kudi a zamanance 'bank transfer' a cikin caji ofis da sauran ofisoshin 'yan sanda a duk fadin kasar.

Hakan ya biyo bayan zarge-zargen da ke tasowa cewa ana hada-hadar kudi ta hanyar amfani da na'urar POS ko 'transfer' da sa hannun wasu bare-gurbin  'yan sanda.

Wannan haramci dai na da nufin kare kima da martabar aikin 'yan sanda da hana yunkurin karbar cim hanci a duk ofisoshin 'yan sanda na kasar.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce babban sufeton 'yan sanda na kasa IGP Kayode Egbetokun ya ja kunnen masu aikata hakan cewa za su kuka da kansu idan aka kama su.

Post a Comment

Previous Post Next Post