'Yan sanda sun dakile yunkurin satar wata mata da mijinta a Katsina


Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da cewa ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da miji da mata a kauyen Hayan Dam na karamar hukumar Kankara ta jihar.

A cikin wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Aliyu Abubakar Sadiq ta ce babban ofishin 'yan sandan karamar hukumar Kankara ya samu labarin cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne dauke da muggan makamai sun mamaye gidan Kabir Magaji da zummar yin garkuwa da shi da matarsa Sa'adatu Magaji.

Bayan samun wannan bayani, 'yan sanda suka gaggauta kai dauki, suka dakile yunkurin, yanzu haka su na kokarin kama wadanda ake zargi.

Sanarwar ta shawarci al'umma da su ba da bayanai ga duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga ganin yadda wasu 'yan ta'addar suka sha da kyar da raunuka a jikinsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp