NDLEA ta gana da masu Otal a Katsina don dakile safarar miyagun kwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta jihar Katsina ta sanar da ganawa ta musamman da masu otal-otal a jihar don tattauna yadda za a dakile safarar miyagun kwayoyi a jihar.

Kwamandan hukumar Hassan Sani Abubakar a cikin wata sanarwa, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa a hankalin a hankali mutane na amfani da otal-otal domin gudanar da haramtaccen kasuwancin cinikin muggan kwayoyi.

Kwamandan a sanarwar da kakakin hukumar Bashir Adamu ya aike wa DCL Hausa, ya ja kunnen cewa hukumar ba za ta yi kasa guiwa ba wajen kakkabowa tare da zakulo wadanda ke da hannu a wannan batu don hukunta su daidai da doka.

Ya ce za su yi duk mai yiwuwa don ganin otal-otal a jihar Katsina ba su zamo mafakar masu haramtaccen kasuwancin miyagun kwayoyi ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp