Tinubu ya haramta wa ministocinsa tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umurnin haramta wa ministocinsa da sauran mukarraban gwamnatinsa tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Shugaba Tinubu ya ba da umurnin ne ta cikin wata wasika da shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, ya aike wa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
A cikin wasikar, mai kwanan wata 12 ga Maris, 2024, Tinubu ya ba da umurnin hana duk wasu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Sai dai ya ce an keɓance tafiyar da ta zama wajibi.