Ban yarda da zargin da gwamnatin Tinubu ta yi ga waɗannan bayin Allah ba

Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi yana ƙalubalantar gwamnatin Najeriya bisa zargin wasu da aka fitar da jērin sunayen su cewa suna da hannu dumu-dumu a ayyukan ta'addanci a ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar da ke tattara bayanan sirri kan ilahirin harkokin da suka jībanci kudade a faɗin ƙasar, ta fitar da bayanai dake nuni ga wasu ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni har ma da masu harkar canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare da hannu wurin tallafawa ayyukan ta'addanci, musamman da kuɗaɗe.

Sheikh Ahmad Gumi ya ce jami'an tsaro basu da hurumin aiyana wani a matsayin mai tallafawa taaddanci da kuɗaɗe saboda a cewar sa 'yan ta'addan su ke ɗaukar nauyin kansu da kansu, ta amfani da kuɗaɗen fansa da suke samu idan suka yi garkuwa da mutane.

Malamin addinin a baya-bayanan ya bukaci gwamnatin Najeriya ta basu damar tattauna wa da yan ta'adda da suka sãce ɗalibai kusan ɗari uku garin Kirga dake jahar Kaduna, saboda da yace da alama abin zai yi matuƙar wahala ga jami'an tsaro, yana mai cewa bai kamata a  zuba idanu ana gani shugaba Tinubu ya maimaita irin kurakurai da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yai ba, na ƙin yin sulhu da 'yan fashin na dãji.

Post a Comment

Previous Post Next Post