Katsina za ta karbi bakuncin taron inganta tsaro da zaman lafiya na shiyyar arewa maso yamma


Gwnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da hadin guiwa tsakanin gwamnatin jihar da shirin bunkasa kasashe na majalisar dinkin duniya UNDP su karbi bakuncin taron inganta tsaro da samar da zaman lafiya a shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya a jihar Katsina.

Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Barr Abdullahi Garba Faskari ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da kwamitin tsare-tsaren yadda za a karbi bakuncin a madadin Gwamnan.

Taken taron shi ne dabarun inganta tsaro da zaman lafiya: shawo kan matsalolin ayyukan ta'addanci da sauyin yanayi.

Kwamitin na kunshe da mambobi 14 da Sakataren Gwamnatin jihar ne shugaba, sannan akwai shugaban ma'aikatan jihar Katsina da kwamishinonin yada labarai da na tsaro da lamurran cikin gida da kuma na shari'a.

A cikin wata sanarwa daga daraktan yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Aliyu Yar'adua, ta ce daga cikin nauyin da aka dora wa kwamitin akwai hada hannu da shirin UNDP da sauran hukumomin da suka dace don karbar bakuncin taron yadda ya dace a Katsina.

Kazalika, kwamitin zai shiga ya fita don ganin an saukaka zirga-zirga ga bakin da za su halarci taron, samar da wurin da Taron zai gudana, gayyatar baki da sauran abubuwan da suka shafi wannan taro.

Post a Comment

Previous Post Next Post