Wasu daga cikin maniyyata a Nijeriya,sun nemi a maido musu da kudaden su.

 Wasu daga cikin maniyyata a Nijeriya sun bukaci da amayar musu da kudaden su da suka biya.


Biyo bayan matakin da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta dauka na kara  kudin aikin hajjin shekarar 2024 da naira miliyan 1.9, da dama daga cikin mahajjatan j sun bukaci hukumar jin dadin alhazai ta jihar da ta mayar musu da kudaden da suka ajiye.



Wannan dai na zuwane a daidai lokacin da  kungiyoyin fararen hula da masu ruwa da tsaki a Nijeriya, suka yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dubi halinda maniyyata hajji bana ke ciki don samun mafita.


A ranar Lahadin da ta gabata ne NAHCON ta kara kudin aikin hajjin bana zuwa kasar Saudiyya da N1, 918,032.91 yayin da ta tsayar da ranar 28 ga Maris, 2024 a matsayin ranar da za'a kammala biyan wannan kudi.


 A watan Disambar shekarar 2023 ta kayyade farashin hajjin bana da Naira miliyan 4.9 bisa tashin farashin canji.


Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata, hukumar ta bukaci wadanda suka biya kudin farko da su kara Naira miliyan 1.9, inda adadin ya kai Naira miliyan 6.8.


Wannan yasa wasu daga cikin maniyyatan suka bukaci Hukumar Kula da aikin hajji ta jihohi da su mayar musu da kudaden da suka biya a baya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp